
Blurb
Ba a yi mu domin rayuwan Kaɗaici ba: An shirya domin zumunci cikin duniya cike da kaɗaici: A Love God Greatly Hausa Bible Study Journal
Product Code:
9798211428317
ISBN13:
9798211428317
Condition:
New
$15.62

Ba a yi mu domin rayuwan Kaɗaici ba: An shirya domin zumunci cikin duniya cike da kaɗaici: A Love God Greatly Hausa Bible Study Journal
$15.62
Ba a yi mu domin rayuwan kaɗaici ba. Ba'a taɓa yin wata tsara a tarihi wanda suke iya magana da juna cikin kankanin lokaci kamar wanann tsran mu, amma duk da haka dayawa daga cikin mu na jin kamar mu na zaman kaɗaici. Ko ba mu da aure ko mu na da aure, ko karami ko babba, ko wanda ba ya magana ko mai yawan surutu, ko mai kuɗi ko mai talauci, duk an halice mu da son a kaunace mu kuma a san mu. Tun daga farko a gonar Aidan, mun gan yadda Allah Ya kera mu mu yi rayuwa cikin zumunci da Shi da juna kuma. Amma zama cikin zumunci na da wuya. A yau dayawa daga cikin mu na ɗaukan lokaci da dama a zaune a gaba wata screen fiye da zama da abokai ko iyali. Da gaske mu na da "abokai" da dama kan yanan gizo amma Allah Ya halice mu domin zumunci fiye da a gaban screen. Ba ma kaɗai zumunci haka kawai ba amma zumunci a wurare ta musanman a cikin rayuwan mu. A cikin wannan bincike na tsawon mako huɗu, za mu sa hankali kan yadda Allah Ya halice mu domin zumunci da Shi, da iyalin mu da abokan mu da Iklisiyan mu da duniya duka. Gaskiya ne za mu ji kamar mu kaɗai ne kuma an bar mu haka, amma bai kamata mu yi rayuwa haka ba. A cikin wannan binciken, za mu koya menene yadda a ke zumunci a cikin Littafi mai Tsarki da kuma yadda za mu iya amfani da shi a cikin rayuwan mu. Rayuwa ya wuce kaɗaici. Mu haɗa kai domin yin wannan binciken tare da naki littafi, ko ta yanan gizo, ko kan app na mu na Love God Greatly. Za ki samu abubuwan da su ka shafe Ba a yi mu domin rayuwan Kaɗaici ba har da rubuce rubuce na kullum da jama'a kan yanan gizon mu yayinda mu ke tafiya cikin me ake nufi da yin rayuwa cikin zumunci kamar na Littafi mai Tsarki.
Author: Love God Greatly |
Publisher: Blurb |
Publication Date: Aug 23, 2024 |
Number of Pages: 136 pages |
Binding: Paperback or Softback |
ISBN-10: NA |
ISBN-13: 9798211428317 |